in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da ba da taimakon jin kai ga gamayyar kasa da kasa
2013-12-13 16:05:49 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi, ya bayyana cewa aikin ba da taimakon jin kai ga gamayyar kasa da kasa, na daya daga cikin manyan ayyukan ba da agaji ga kasashen ketare da kasar Sin ke aiwatarwa.

Mr. Liu wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis 12 ga watan nan yayin babban taron MDD karo na 68, inda aka tattauna matakan karfafa batun ba da agaji, da kuma taimakon jin kai na MDD.

Zaunannen wakilin kasar ta Sin ya kuma bayyana cewa, cikin 'yan shekarun nan, ta hanyar hadin gwiwa tsakanin ta da ragowar kasashen duniya, kasar Sin ta ba da taimakon jin kai na gaggawa da na dogon lokaci, musamman ga kasashe masu fama da rigingimu dake yankunan nahiyoyin Asiya, da Afirka, da Gabas ta Tsakiya da kuma yankin Caribbean da dai sauransu. Tana kuma ba da irin wannan taimako ba tare da gindaya wani sharadi ba, wanda hakan ya yi daidai da tsarin hadin gwiwar tattalin arziki na kasashe masu tasowa.

Mr. Liu ya kuma kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da mai da hankali kan yanayin ba da taimakon jin kai na kasa da kasa, tare da ci gaba da ba da taimakon kudi ga Asusun ba da taimako ga al'amuran ba-zata na MDD, da kuma ofishin kula da harkokin jin kai na MDD, don ba da gudumawar ta ga wannan muhimmin aikin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China