in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Red Cross ya nuna damuwa kan halin da fararen hula ke ciki a Syria
2014-01-14 15:58:17 cri

Rikicin Syria dake taba miliyoyin fararen hula, wani bala'i ne dake ba da tsoro a yayin da taimakon jin kai ya kasa isa, in ji shugaban kungiyar agaji ta Red Cross ICRC mista Peter Maurer a ranar Litinin.

A cewar ICRC, a yayin ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Syria, mista Maurer ya gana da jami'an gwamnatin Syria, kuma ya nemi hukumomin kasar da su ba da taimakon jin kai ga mutanen da suke cikin bukata.

Mista Maurer ya sadu da iyalan da rikicin kasar ya tilasta su kaura zuwa yankin sansanin Damascus, shugabanni da ma'aikatan sa kai na Red Cross ta kasar Syria. "Babu wani abun matsalar jin kai na kara tabarbarewa a kasar Syria." in ji mista Peter Maurer tare da bayyana cewa, yana cikin damuwa sosai da halin da fararen hula suke ciki, tare da fadawa cikin tarkon tashe-tashen hankali dake kawo jinkiri ga aikin jin kai.

Haka kuma babban jami'in na ICRC ya bayyana cewa, mutane suna bukatar magunguna, abinci da sauran kayayyakin jin kai, ya kuma jaddada kan matsalolin da ICRC ke fuskanta, musamman ma a yankunan dake hannun masu adawa da gwamnatin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China