Shugaba Xi ya shaida wa tawagar karkashin jagorancin mataimakin firaminista na farko kana ministan harkokin wajen kasar Kuwait Sheikh Sabah Khaled al-Sabah cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bunkasa dadaddiyar abokantakar da ke tsakanin sassan biyu, kuma kamata ya yi sassan biyu su kara karfafa tsare-tsare da fadada hadin gwiwarsu.
A dangane da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya da yankin Gulf kuwa, shugaba Xi ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kokarin da mambobin kasashen na GCC suke yi na kare cikakkun yankunansu da zaman lafiya na shiyyar. Ya ce, har ila yau, kasar Sin za ta goyi bayan GCC bisa rawar da take takawa a harkokin duniya da na shiyya-shiyya.
A nasa jawabin, Sheikh Sabah ya isar da sakon fatan alherin mambobin kungiyar ga shugaba Xi Jinping da kuma al'ummar kasar Sin, yana mai cewa, mambobin kungiyar ta GCC suna dora muhimmanci sosai kan dangantakarta da Sin, kuma a shirye suke su kara karfafa dangantakar abokantakarsu daga dukkan fannoni.(Ibrahim)