Shugaban ya ce, kare jam'iyyar daga wannan mummunan al'ada a tsawon shekarun da ta yi tana mulki a kasar, yana daga cikin babban burinta na siyasa, kuma wajibi ne a aiwatar da aikin yadda ya kamata.
Xi Jinping wanda shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, ya bayyana hakan ne yayin zaman taro na uku na hukumar ladabtarwar babban kwamitin tsakiya na JKS.
Ya ce, kamata ya yi dukkan manyan jami'an su mutunta dokokin jam'iyya, kana su kwana da sanin cewa, duk wanda aka kama da laifin cin hanci, to zai yabawa aya zaki.
Ya kuma shaida wa mahalarta taron cewa, majalisar wakilan jama'a ta kara tsaurara matakan sa-ido kan yadda wasu ke amfani da mukamansu tare da fadada kofofinta na bincikin kan hanci tsakanin jami'an gwamnati, matakin da shugaban ya ce, ya haifar da sakamako mai kyau daga jama'a. (Ibrahim Yaya)