in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya bayar da lambobin yabo a fannonin kimiyya da fasaha
2014-01-10 15:50:20 cri

A ran 10 ga wata da safe ne, kwamitin tsakiya na JKS, da kuma majalisar gudanarwa ta kasar Sin suka shirya wani taro cikin hadin gwiwa don ba da lambobin yabo ga wadanda suka kware a fannonin kimiyya da fasaha. Shugabannin kasar Sin da JKS, Xi Jinping da Li Keqiang da dai sauransu sun halarci taron kuma sun bayar da lambobin yabo ga kwararrun.

A gun taron, an bayar da lambobin yabo ga kwararru 10 da nasarorin da aka samu daga ayyuka da yawansu ya kai 313 a shekara ta 2013. Haka kuma an bayar da lambar yabo ta koli ta Sin a fannonin halittu, da fasahohi, da ci gaban kimiyya da fasahohi, da hadin kai da kasashen waje.

A madadin kwamitin tsakiya na JKS, da kuma majalisar gudanarwa, Mista Li Keqiang ya yi jawabi a gun taron, inda ya bayyana cewa, a halin yanzu dai kasar Sin tana cikin wani lokaci mai muhimmanci matuka wajen kafuwar wata kasa mai kere-kere. Wajibi ne a mai da hankali kan harkokin kere-kere na kimiyya da fasaha, sa'an nan kuma za a kara daga masana'antu zuwa matsayin koli da matsakaici da karfafa ingancin tattalin arziki, da kuma samar da fiffiko don yin takara a duk duniya, da habaka bunkasuwar Sin, da daidaita kalubalen da ake fuskanta a bangaren makamashi da muhalli, da samun bunkasuwa cikin dogon lokaci.

Li ya kara da cewa, ya kamata a hada batun kere-keren kimiyya da fasaha tare da bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma. A mayar da kere-keren kimiyya da fasaha zuwa wani matsayi mai muhimmanci wajen raya kasa, kara yin hangen nesa da hadin kai da yin mu'ammala da sauran kasashen waje, don koyon kyawawan nasarorin da sauran kasashen suka samu, ta yadda za a iya sa kaimi ga samun sakamako mai yawa a fannonin kimiyya da fasaha, da bayar da gudummawar Sinawa ga cin gaban kimiyya da fasaha na bil-Adam. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China