A yayin ganawarsu, shugaba Xi ya bayyana cewa, a matsayin muhimman kasashe masu tasowa da kuma kasashe masu karfin bunkasa tattalin arziki, dangantaka tsakanin Sin da Afirka ta Kudu ta bunkasa yadda ya kamata, wadda ta yi babbar tasiri ga bunkasa dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka da zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya. A don haka yana fatan bangarorin biyu su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, domin sa kaimi ga ciyar da dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka zuwa wani sabon mataki.
A nasa bangare, mista Motlanthe ya bayyana cewa, kasar Afirka ta Kudu na fatan tabbatar da matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma tare da kasar Sin, a kokarin kyautata tsarin hadin gwiwa tsakaninsu, da zurfafa hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, cinikayya, al'adu na bil'adam da sauransu, ta yadda za su kara taimakawa juna kan harkokin duniya da na shiyya shiyya, da zummar bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki.(Fatima)