Rahoton ya yi kiyasin cewa, a bana saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya zai karu zuwa kashi 3.2 bisa dari daga kashi 2.4 bisa dari a shekarar bara, sa'an nan a shekarar 2015, adadin zai karu zuwa kashi 3.4 bisa dari.
Bugu da kari, rahoton ya nuna cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasashe masu tasowa a shekarar bana da badi zai kai kashi 5.3 bisa dari da kashi 5.5 bisa dari, wadanda za su zarce adadin shekarar bara na kashi 4.8 bisa dari. (Amina)