Gwamnatin kasar Somaliya, ta bayyana shirinta na sake bude jami'ar kasar da aka rufe na tsawon lokaci, sakamakon fadan da ake yi a kasar.
Mahukuntan kasar sun bayar da wannan sanarwar ce a ranar Alhamis 14 ga wata, bayan da majalisar ministocin kasar ta amince da shirin sake bude jami'ar kasar, yayin taronta na mako-mako, wanda firaministan kasar Abdi Farah Shirdon ya shugabanta.
Firaministan ya fada cikin wata sanarwa cewa, ilimi shi ne abin da ke kan gaba cikin ajandar ko wace kasar da ta waye kamar kasar Somaliya, domin ta hanyar ilimi ne za a yaki talauci, jahilci tare da inganta rayuwar jama'a.
Bayanai na nuna cewa, an kafa jami'ar kasar ta Somaliya ce a shekara ta 1974, tana da tsangayoyi 13 da malamai 700 da dalibai sama da 15,000, kafin daga bisani yakin basasar kasar ya kai ga lalata ta.
Tuni dai ministan inganta rayuwar jama'a da ayyukan gwamnati, ya kaddamar da kamfel din ganin yara sun koma makaranta, ta yadda daliban kasar ta Somaliya miliyan 1 za su koma makaranta a cikin shekaru 3 masu zuwa. (Ibrahim)