in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya gana da tsohon firaministan Ingila game da nagartaccen ilimi
2013-09-10 10:29:40 cri

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gana da tsohon firaministan Ingila Gordon Brown a ranar Litinin din nan, wanda ya je kasar domin tattauna yadda za'a inganta samar da ilimi mai kyau a matsayin shi na manzo na musamman na MDD a kan ilimi.

Shugaban na Najeriya Jonathan a lokacin ganawar ta su ya tabbatar da kudirin gwamnatinsa na ganin ta aiwatar da manufofin da za su samar da ilimi nagartacce, wadanda suka hada da amfani da kudin da Amurka ta yi alkawarin za ta samar na dala miliyan 250 a matsayin tallafi.

Mr. Jonathan ya ce, samar da ilimin zai ba da kafa ga matasa su samu dabaru da fasashar da ake bukata wajen samun fasashohin da ake bukata a wajen ayyuka tare da ba su damar yin takara da juna sosai, sannan kasar za ta samar da duk wani taimako da ya kamata ga gwamnatocin jihohi domin ganin sun samu damar amfana daga kudin tallafin da za'a samu su kuma yi amfani da su yadda ya kamata.

Tun da farko a cikin jawabinsa, Mr. Gordon Brown ya ce, kafin ganawarsa da shugaba Jonathan, ya riga ya yi tattaunawa mai ma'ana da mataimakin shugaban kasar Mohammed Namadi Sambo da kuma minista mai kula da tattalin arziki da sha'anin kudi Ngozi Okonjo-Iweala.

Mr. Brown ya ce, ganawarsa da manyan jami'an gwamnatin Najeriya ta mai da hankali ne a kan gudumuwar da za'a samu daga kasashen waje domin ba da damar samar da ilimi ga matasan Nigeriya, a yi bayanin cewa, MDD da sauran kungiyoyi masu ba da taimako a shirye suke na taimakawa a cimma wannan aniya ta gwamnatin tarayyan Nijeriya da na jihohin domin sun fadada samar da sanin makaman aiki ga malaman makarantu.

MDD za ta kuma taimaka wajen inganta ilimin 'ya'ya mata da kuma ganin an samar da kafar amfani da ababen koyarwa na ilimin fasahar zamani kamar littafan karatu na yanar gizo, da na'urorin masu kwakwalwa, ta yadda za'a samar da ilimi ga matasa yadda ya kamata, in ji manzon na musamman. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China