Firaministan kasar Sin Li Keqiang a lokacin ziyararsa ranar Litinin 9 ga wata, ya gana da malaman makarantu a birnin Daliang na jihar Liaoning, gabannin bikin ranar malamai ta kasar Sin a ranar 10 ga Satumba, inda ya jaddada bukatar daga darajar ilimi a yankunan da ba su ci gaba ba.
Lokacin da yake zantawa da malaman, ya mika sakon fatan alheri ga daukacin malamai na kasar Sin inda ya kira aikin koyarwa a wani sana'a mai daraja har abada.
Mr. Li ya karfafa gwiwwa ga sauran al'ummomi da su dauki fannin koyarwa a yankunan da ba su cigaba ba sosai a yammacin kasar Sin, sannan ya yi kira da a samar da karin gurabe ma malamai daga yammacin kasar su samu horo a gabashin kasar domin darajar ilimi ya inganta a yankunan nasu a kuma yaye talauci da ya addabi daliban domin su samu wani fata na samun ilimi.
Firaministan har ila yau ya lura cewa, ilimi nagartacce shi ne mabudin da zai rage tazara tsakanin kauyuka da birane a cikin yankuna kasar, don haka ya bukaci a rika ba da fifiko wajen ba da kayayyakin samar da ilimi ga wadannan yankuna da ba su cigaba ba sosai fiye da sauran yankuna a kasar. (Fatimah)