Liu Jieyi ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu, ana gudanar da aikin lalata makamai masu guba na kasar Syria cikin yanayi mai kyau, kuma an riga an kammala matakin farko na aikin fitar da sinadaran makamai masu guba daga kasar Syria zuwa ketare, kasar Sin tana maraba sosai da lamarin.
Mr. Liu ya kuma bayyana cewa, hanyar siyasa ita ce hanyar da ta fi dacewa wajen warware batun Syria. Kasar Sin tana maraba da za a yi taron Geneva karo na biyu a ran 22 ga watan Janairu. Ko da yaushe kasar Sin tana mai da hankali sosai kan yanayin siyasa na kasar Syria, kuma za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da bangarori daban daban da abin ya shafa, don samun sakamako mai gamsarwa a taron Geneva karo na biyu, za ta kuma ci gaba da taka rawarta wajen warware batun Syria yadda ya kamata. (Maryam)