Babban sakatare na MDD Ban Ki-moon ya bayyana a ranar Litinin cewa, aikin share fagen taron kasa da kasa da kowa ke jira zai taimaka wajen warware rikicin kasar Syria ta hanyar siyasa na bisa hanya mai kyau, tare da jaddada cewa, shawarwari sun kasance hanya guda domin kawo karshen zubar da jini a cikin wannan kasa.
Taron kasa da kasa kan Syria zai gudana a Monteux, sannan kuma a Geneva daga bakin ranar 22 ga watan Janairu mai zuwa.
A yayin wani taron manema labarai da aka shirya a ranar Litinin a cibiyar MDD dake birnin New York, mista Ban ya bayyana fatansa na ganin cewa, batun halartar kasar Iran a wannan taro, za'a warware shi cikin gaggawa.
Ya kamata ta ba da taimako ga zaman lafiyar Syria tare da sauran kasashen dake wannan shiyya. Iran babbar kasa ce a wannan yanki da za ta iyar kawo muhimmin taimako. Ke nan ya zama wajibi kasar Iran ta halarci wannan taro kamar sauran kasashe, in ji shugaban MDD.
Ban da MDD, kasashe masu hurumin halarta wannan su ne mambobin din din din na kwamitin tsaro da suka hada da Sin, Faransa, Rasha, Burtaniya da Amurka. Haka kuma akwai kungiyar tarayyar Larabawa, tarayyar Turai, kungiyar kasashen dangantakar musulunci da sauran wasu kasashe 26. (Maman Ada)