Kakakin rundunar sojojin tekun kasar Sin Liang Yang ya bayyana a Talata 31 ga watan Disamba na shekarar 2013 cewa, jirgin ruwan soja na kasar Sin ya riga ya kama hanyar zuwa tekun Mediterranean, don kare jiragen ruwan da ke jigilar makamai masu guba na kasar Syria.
Bayan da wannan jirgin ruwan sojan kasar Sin ya isa tashar jiragen ruwa na Limassol dake kasar Cyprus, zai hadu da jiragen ruwan soja na sauran kasashe, sa'an nan kuma za su fara ayyukansu, a kokarin da ake yi na lalata makamai masu guba na kasar Syria. (Maryam)