A wannan rana, Ms. Kaag ta yi bayani kan aikin lalata makamai masu guba na kasar Syria da kuma kalubalolin da ake fuskanta ga kwamitin sulhu na MDD.
Ta ambaci wasu matsalolin da aka gamu da su yayin gudanar da wannan aiki, kamar rikice-rikicen kasar Syria, wahalar lalata makaman da kuma canjin yanayi ba zato ba zamani da dai sauransu, amma ta yi imani cewa, a halin yanzu, an shirya sosai wajen gudanar da wannan aiki, kuma an riga an samu kudaden da ake bukata, jigilar sinadaren makamai masu guba karo na farko daga kasar Syria zuwa katere a ran 7 ga wata, shi ne muhimmin mataki da aka kammala dangane da wannan aiki.
A ran 7 ga wata ne, an fitar da sinadaren makamai masu guba na kasar Syria karo na farko daga tashar jiraren ruwa na Latakia dake kasar cikin wani jirgin ruwa na kasar Denmark, wannan shi ne mafarin ayyukan lalata makamai masu guba na kasar ta Syria. Inda kuma jigaren ruwan soja na kasashen Sin, Denmark, Norway da kuma Rasha suka yiwa wannan jirgin ruwa mai dauke da makamai rakiya a kan teku. (Maryam)