Ministan harkokin wajen kasar Syria Walid al-Moallem, ya bayyana a ranar Lahadi cewa, kasarsa na dukufa wajen ganin halartar kasar Iran a taron Geneva karo na biyu kan zaman lafiya a kasar Syria, tare da nuna cewa, babu wata hujja na janye Iran bisa wasu dalilan siyaya dake shafar Amurka da 'yan adawar Syria dake kasashen waje.
Amurka da 'yan adawar Syria dake ketare sun tsayin gwamin jaki kan batun halartar Iran a taron Geneva na biyu.
Kusan kasashe 30 za su halarci wannan taro da aka tsai da shiryawa a ranar 22 ga watan Janairun sabuwar shekara a birnin Montreux na kasar Swiss, tare da kuma shawarwarin da za'a fara a ranar 24 ga watan Janairu a birnin Geneva tsakanin wakilan gwamnatin Syria da bangaren 'yan adawar Syria.
Manzon musamman na MDD da tarayyar kasashen Larabawa kan kasar Syria, Lakhdar Brahimi, ya tunatar a baya bayan nan cewa, Amurka har yanzu ba ta yi imani ba kan halartar Iran a wadannan shawarwari na Geneva.
Har ila yau, ministan harkokin wajen kasar Syria ya jaddada cewa, kasarsa tana gaggawar ganin taron Geneva na biyu ya gudana, domin kasar Syria na da hange mai haske dake dogaro da bukatun al'ummar Syria da niyyar kasar bisa jagorancin shugaba Bashar al-Assad.
Ministan harkokin wajen Syria ya yi wadannan kalamai ne a ranar Lahadi a yayin wani zaman taron kara wa juna sani na kwanaki biyu da ya gudana a birnin Damascus kan kalubale da nauyin kafofin watsa labarai a cikin halin da kasar take ciki yanzu. (Maman Ada)