in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya koka game da karuwar tashin hankali a Syria
2013-12-27 10:12:24 cri

A ranar Alhamis ne babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya bayyana damuwa matuka kan yawaitar tashin hankali a kasar Syria, inda ya yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, da su mayar da hankali wajen warware rikicin ta hanyar siyasa yadda ya kamata.

Mr. Ban ya koka ne cikin wata sanarwa da kakakinsa ya bayar, yana mai cewa, ya damu da yadda rikici ke kara karuwa a Syria a 'yan kwanakin nan, musamnan a garin Aleppo, inda rahotanni ke cewa, an halaka fararen hula da dama, baya ga wasu da suka jikkata.

Babban sakatare na MDDr, ya kuma yi allahwadai da yadda ake ci gaba da amfani da manyan makamai da rokoki barkatai kan yankunan fararen hula. Ya kuma jaddada cewa, wajibi ne dukkan bangarorin da ke gwabza fada, da su mutunta dokokin kare hakkin bil adama da na jin kai na kasa da kasa, tare da kare rayukan fararen hula a ko wane irin yanayi.

Yanzu dai ana nan ana shirye-shiryen gudanar da taron kasa da kasa game da Syria a Geneva daga ranar 22 zuwa 24 ga watan Janairun shekara ta 2014, inda gwamnatin Syria da 'yan adawa za su gana a karon farko a hukumance don tattauna hanyoyin samar da zaman lafiya a kasar.

Bayanai na nuna cewa, za a bude kashi na farko na taron ne a Montreux na kasar Switzerland, kana daga bisani a garzaya ofishin MDD da ke Gevena. Manufar taron, ita ce warware rikicin kasar ta hanyar siyasa, inda za a cimma wata yarjejeniya tsakanin gwamnati da 'yan tawaye, ta yadda za a aiwatar da sanarwar ta Geneva da aka cimma a taron kasa da kasa na farko game da batun a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2012,wadda ta yi kiran da a kafa gwamnatin wucin gadi da za ta jagoranci shirya zabuka a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China