Ministan watsa labarai na kasar Syria Omran al-Zoubi, ya bayyana cewa, gwamnatin Syria za ta halarci taron Geveva karo na biyu ba tare da wani rufa-rufa ba.
Ministan ya bayyana hakan ne ranar Laraba, yayin da yake zantawa da gidan talabijin na kasar, inda ya jaddada kudurin gwamnatin kasar ta Syria na halartar taron zaman lafiyar da za a yi a Geneva da nufin bullo da matakan siyasa da za su kai ga warware rikicin kasar.
Ko da yake, ministan ya ce, wasu bangarori na kokarin kawo kafar ungulu ga taron, inda suke kokarin cusa batun tattaunawa tsakanin Iran da kasashen yamma game da shirinta na nukuliya a taron na Geneva.
Al-Zoubi ya ce, gwamnatin Syria ba ta damu da sharuddan da 'yan adawa suke son gindiyawa ba, yana mai cewa, 'yan adawar kasar da ke ketare ba su da wani shirin na siyasa.
Ya ce, 'yan adawar sun canja shawarar halartar taron zaman lafiyar ne da wakilan gwamnati saboda matsayin lamba daga iyayen gidansu na kasashen yamma. (Ibrahim)