in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi Allah wadai da ziyarar firaministan Japan a wurin ibada na Yasukuni
2013-12-26 15:55:24 cri

Mahukuntan kasar Sin sun yi Allah wadai da ziyarar baya bayan nan, da firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya kai wurin ibadar nan na Yasukuni, matakin da Sin din ke kallo a matsayin abin da ka iya sake haifar da cikas, ga mawuyacin halin da dangantakar kasashen biyu ke ciki.

Da yake tsokaci kan wannan lamari, jim kadan da ziyarar ta firaminista Abe a makabartar ta Yasukuni, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya ce, hakan na nuna yadda mahukuntan Japan din ke karrama wadanda suka aikata laifukan keta martabar bil'adama, ba tare da la'akari da tasirin hakan, ga iyalan wadanda yakin duniya na biyu ya shafa a nahiyar ba.

Qin Gang ya kara da cewa, matakan nuna kin jinin wasu yankuna da Japan ta nuna a baya, sun haifar da aukuwar manyan laifuka ga kasar Sin, da ma sauran kasashen dake nahiyar Asiya, baya ga matsalar da hakan ya haifar ga al'ummar ita kan ta kasar ta Japan. Don gane da ziyarar ta Abe a wurin ibadar na Yasukuni, Mr. Qin ya ce, wakilan ofishin ma'aikatar waje, da manzon kasar ta Sin a Japan, za su tuntubi jakadan kasar Japan dake nan Sin da kuma ma'aikatar wajen kasar ta Japan.

Wannan ne dai karon farko da firaministan kasar Japan mai ci ya ziyarci wurin ibadar na Yasukuni tun bayan shekarar 2006. A baya ma dai ziyarar shekara-shekara da tsohon firaministan kasar ta Japan Junichiro Koizumi ya rika kaiwa wannan wuri tsakanin shekarun 2001 zuwa 2006, sun kasance manyan dalilan tsamamar dangantaka tsakanin Japan da kasashen dake makwaftaka da ita. Tuni kuma kasar Koriya ta Kudu ta yi kashedin cewa, wannan ziyara ta firaminista Abe na iya kara dagula dangantakar Japan da kasashe makwafta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China