Wurin ibadar Yasukuni dai wuri ne da aka kebe kaburburan masu laifukan yaki, ciki hadda wadanda suka jagoranci dakarun kasar yayin yakin duniya na biyu.
Don gane da ziyarar firaministan kasar ta Japan a wannan wuri, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya bayyana cewa, Sin ta yi Allah wadai da hakan, kuma kamata ya yi kasar Japan ta girmama ra'ayin kasar Sin, da ma sauran kasashen Asiya wadanda yakin duniyar na biyu ya shafa kan wannan batu.
Har ila yau a dai wannan rana, yayin da ya ke tsokaci kan batun, kakakin gwamnatin kasar Koriya ta Kudu Liu Zhenlong, ya sanar da cewa firaministan kasar Japan, ya kai ziyara Yasukuni ba tare da la'akari da damuwar gamayyar kasashe makwabtansa ba, wanda hakan ya sa gwamnatin Koriya ta Kudu ta yi kakkausan suka ga ziyarar ta sa.
Bugu da kari, ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Janpan ya ba da wata sanarwa a ran 26 ga watan, dake cewa, ziyarar Mr. Abe a wurin ibada na Yasukuni, za ta haifar da barazana ga dangantakar abokantaka dake tsakanin gwamantin Japan da sauran kasashe makwabtanta. Don haka Amurka ke fatan Japan, za ta iya warware matsalolin dake tsakaninta da sauran kasashe makwabtan ta, ta hanyoyin da za su dace da kyautatuwar dangantakar dake tsakaninsu. (Maryam)