in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar LDP ta samu babban rinjaye a zaben 'yan majalisa a Japan
2012-12-17 15:33:52 cri

Jam'iyyar LDP wato Liberal Democratic Party ta lashe zaben 'yan majalisa na ranar Lahadi a kasar Japan bisa babban rinjaye a zauren majalisa da yawan kujeru 294, a cewar wani sakamakon wucin gadi da aka fitar. Babbar kawar jam'iyyar LDP, wato sabuwar jam'iyyar Komeito ta samu kujeru 31.

Shugaban LDP, tsohon faraminista Shinzo Abe, da ya kamata ya zama sabon faraminista ya bayyana cewa, nasarar da jam'iyyarsa ta samu na da nasaba da dalilin gazawar jam'iyyar demokuradiya dake mulkin kasar tun yau da kusan shekaru uku. Wannnan ya sanya mutanen kasar suka bukaci kawo karshen mulkin jam'iyyar demokuradiya domin haka ne suka jefa kuri'ar kin yarda da jam'iyyar a yayin wannan zabe, in ji mista Abe a yayin wani taron menema labarai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China