in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mai da martani kan ziyarar da 'yan majalisar ministocin Japan suka yi a wajen ibada
2013-10-18 20:38:55 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying a ranar Jumma'ar nan 18 ga wata ta mai da martani a madadin kasar game da ziyarar da 'yan majalisar ministocin kasar Japan suka kai a wajen ibadar Yasukuni, wanda ke da alaka da yakin kai hari a lokacin bikin kaka da suka yi. Madam Hua tana mai kira ga kasar ta Japan da ta yi la'akari game da tarihi domin wannan neman tsokana ne.

Madam Hua ta ce, game da hakan, tuni mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Liu Zhenmin ya mika sammaci ga jakadan kasar Japan din dake nan kasar Masato Kitera domin ya nuna rashin jin dadin kasar da kuma suka da kakkausar murya ga bangaren kasar Japan.

Kakakin ta yi bayanin cewa, wannan wajen ibada wani wuri ne da ake girmama shi da kuma amfani da shi domin tunawa da mazan jiya da suka aikata laifukan yaki tare da cin zarafin al'ummar nahiyar Asiya.

Wannan ya kamata a duba shi saboda yadda dangantaka yake tsakanin Sin da Japan din, in ji madam Hua, wadda ta jaddada matukar rashin jin dadin kasar game da wannan ziyarar da 'yan majalisar ministocin Japan suka kai wannan wurin ibada wanda ke nuna wani yunkuri na wanke kasar ta Japan daga duk wani laifin da ta aikata a cikin tarihi da kuma kalubalantar sakamakon yakin duniya na biyu da dokar bayan yakin da kasashen duniya suka fitar.

Don haka kakakin ta bukaci bangaren kasar Japan din da ya mutunta kalamansu da kokarin da suke yi na nazarin tarihin inda suka mamaye tare da daukan matakan da suka kamata wajen sake samun amincewar makwabtansu dake sauran kasashen nahiyar Asiya da ma kasashen duniya baki daya. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China