in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi suka kan ziyarar ministan cikin gidan Japan a Yasukuni
2014-01-02 10:47:06 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin a ranar Laraban nan 1 ga wata ta yi suka da kakkausar murya game da ziyarar da ministan cikin gida na kasar Japan Yoshitaka Shindo ya kai wajen wurin ibadar nan ta Yasukuni.

Shindo dai a ranar Laraban nan 1 ga wata ya ziyarci wurin ibada na Yasukuni, duk da mummunan sukar da aka yi a lokacin da firaministan kasar Shinzo Abe ya ziyarci wurin a makon da ya gabata.

Wannan ziyarar ta Shindo wata sabuwar tsokanar fada ce ta majalissar zartarwar kasar a game da abubuwan da suka shafi tarihi, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Wannan aiki nashi, in ji madam Hua, ya sake nuna muguwar aniyar kasar Japan na goyon bayan laifukan yaki da sojojin kasar suka aikata, kuma shi ne kalubale ga sakamakon yakin duniya na 2, tare da tsarin kasa da kasa da ya biyo bayan haka.

Kakakin ta kuma bukaci kasar Japan da ta duba tarihi da idon basira domin yin gyara a kuskurenta, tana mai jaddada cewa, Sinawa da sauran al'ummar yankin Asiya ba za su amince da Japan da ta mai da hannun agogo baya ba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China