in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan majalisar Japan sun kai ziyara a hurumi duk da suka da ka ce na ce da ake kan haka
2013-04-23 16:02:28 cri

A ranar Talatar nan, wasu 'yan majalisar dokokin kasar Japan guda 168 suka kai ziyara a hurumin Yasukuni dake birnin Tokyo wanda ya yi kaurin suna, kuma mataki ne da ka iya lalata aminci tsakanin kasar da makwabtanta.

Wannan shi ne karo na farko da yawan 'yan majalisa da suka kai irin wannan ziyara ya haura 100, tun watan Oktoban 2005, in ji kafofin watsa labaran kasar.

Babban mataimakin ministan kudade Shunichi Yamaguchi, babban mataimakin ministan muhalli shinji Inoue da babban jami'in manufofi na jam'iyyar Liberal Democratic Party (LDP) Sanae Takaichi duka suna cikin masu kai ziyarar.

An fara wani bukin bazara na tsawon kwanaki uku ranar Lahadi a hubbaren wanda alama ne na karfin sojojin kasar Japan a yakin duniya na biyu lokacin da mataimakin praminista Taro Aso ya kai ziyara bayan da Mr. Abe ya ba da baiko a madadin praminista.

Maimaita irin wannan ziyara da shugabanni da kuma 'yan majalisar kasar Japan ke yi a wannan hubbare, duk da rashin amincewa da ake nunawa ya zamo wata babbar matsala ga kasar Japan wajen gyara dangantakarta da kasashe dake makwabtaka da ita, musamman kasar Sin da Korea ta Kudu wadanda su ne suka wahala sakamakon mamaye da kasar Japan ta yi masu a lokacin 'yakin duniya na biyu.

Kasar Sin ta nuna korafinta dangane da ziyarar ministotin zuwa hubbaren, inda ta bukaci kasar Japan da ta nuna gaskiyar tarihi dangane da mamayar, da kuma mutunta ra'ayin kasashen da suka wahala sakamakon hakan.

Ministan harkokin wajen kasar Korea ta Kudu Yun Byung-se shi ma ya fasa wata ziyarar da ya yi niyyar kaiwa kasar Japan don nuna kin amincewarsa dangane da kai ziyara da ministocin kasar Japan suka kai hubbaren Yakusuni.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China