A wannan rana, mista Riek Machar ya bayyana cewa, ya amince da yin shawarwari da shugaba Kiir, amma kafin hakan, wajibi ne a saki magoya bayan sa a fannin siyasa. Ya ce, wadannan magoya bayan nashi su ne za su kasance muhimman membobin kungiyar da za ta yi shawarwari da gwamnatin kasar.
Daga bisani, ministan watsa labaru na kasar, Michael Makuei Lueth ya mai da martani cewa, ba za a biya bukatun Mr Machar ba sannan Gwamnatin kasar za ta yi shawarwari da shi ba tare da wani sharadi ba.
Tun da farko a wannan rana, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kira ga kwamitin sulhu na MDD da ta kara tura sojojin kiyaye zaman lafiya 5500 a Sudan ta Kudu, don tallafawa sojojin majalisar kimanin 7000 dake kokarin kiyaye zaman lafiya a kasar a halin yanzu, ta yadda za a samu damar tinkarar barazanar yanayin tsaro da kuma ba da kariya ga fararen hula da ma'aikatan MDD a kasar. (Fatima)