in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan cinikin da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta hanyar yin amfani da kudin RMB zai karu sosai
2013-08-09 16:46:19 cri
A ranar 8 ga wata, a birnin Johnnesberg dake kasar Afrika ta kudu, a gun taron tattaunawa karo na farko na kasuwar saka jari tsakanin kasashen Sin da Afrika ta Kudu, babban manaja na reshen bankin Sin a birnin Johnnesberg Qiu Zhikun ya ce, bayan da cinikin da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya kara habaka, yawan ciniki tsakaninsu da aka yi amfani da kudin Sin RMB zai karu.

Wani jami'in da ke kula da kudin kasashen waje na bankin Nedbank ya ce, a cikin shekaru 15 da suka gabata, yawan karuwar ciniki da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya kai fiye da na sauran yankunan, wannan ya kara kawo bukatar yin amfani da kudin Sin RMB don yin ciniki a tsakaninsu, haka kuma, za a sa masu yin ciniki su rage farashinsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China