A gun taron 'yan jarida da aka shirya a yau, Madam Hua ta yi bayani game da yanayin da ake ciki, tana mai cewa Sin na mu'amala sosai da kasar Sudan ta Kudu da kasashe makwabtanta da kungiyar kasashen Afirka da sauransu, za ta ci gaba da kokarinta tare da bangarori daban daban da abin ya shafa, domin sa kaimi ga bangarorin biyu da suka shiga rikici da su daidaita matsala ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu cikin lokaci.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a kokarin sassauta yanayin da ake ciki a Sudan ta Kudu, kungiyar AU da ta IGAD sun riga sun tura hadaddiyar kungiyar shiga tsakani zuwa kasar, wasu kasashen duniya su ma sun tura nasu manzannin na musamman.(Fatima)