Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, bayan kammala ziyarar kwanaki 3 da ya kawo zuwa kasar Sin, inda ya ce nasarar da kasar Sin ta samu wajen amfani da magungunan gargajiya dana zamani a cibiyoyin kiwon lafiya,shi ne tsarin da ya kamata a yi koyi da shi.
Ministan ya zo kasar Sin ne karkashin laimar dandalin ministocin kiwon lafiya na kasashen Sin da Afirka,wanda aka kafa da nufin bunkasa hadin gwiwa a bangaren kiwon lafiya, da gano sassan da bangarorin biyu suke dora muhimmanci.(Ibrahim)