Qin Gang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin wanda ya furta hakan wajen taron manema labarai ya ce, kin amincewar hakan ya biyo bayan sharuddan da kungiyar adawa ta kasar Syria wato SNC ta gindaya kafin ta halarci wannan babban taron sulhu.
Sin, in ji shi, a kullum ta yi imani cewa, ta hanyar siyasa ne kadai za'a iya bi a sulhunta wannan matsalar ta Syria, wanda kuma sauran kasashen duniya ma suka lura da hakan.
Qin Gang ya yi bayanin cewa, yana da matukar muhimmanci ga dukkan bangarorin su goyi bayan kokarin wakilin magatakardar MDD Ban Ki-Moon da manzon musamman na kungiyar tarayyar kasashen Larabawa da MDD Lakhdar Brahimi, a kokarin ganin ko wane ya shiga cikin taron Geneva karo na 2 ba tare da wani sharadi ba.(Fatimah)