A cikin sanarwar, an ce, a wannan rana, an fara kwashe wasu ma'aikatan UNMISS daga birnin Juba, babban binrin kasar Sudan ta Kudu, zuwa birnin Entebbe na kasar Uganda, kuma sauran ma'aikatan UNMISS za su ci gaba da ba da taimako ga fararen hula kimanin dubu 20 da ke neman mafaka a ofishin UNMISS dake birnin Juba. Ban da wannan kuma, a wannan rana kuma, za a kwashe wasu ma'aikatan na MDD daga birnin Bentiu, hedkwatar jihar Unity da ke kasar Sudan ta kudu.
Ban da wannan kuma, sanarwar ta ce, UNMISS za ta ci gaba da yin kokari tare da kasashen duniya da shiyya-shiyya, don lalubo bakin zaren warware batun kasar. Idan al'amura suka inganta a kasar, za a dawo da ma'aikatan da suka janye daga birnin Juba. Ban da wannan kuma, UNMISS ta yi shirin kara jibge sojoji a garuruwan Bor, Bentiu don tabbatar da tsaron jama'a.
A wannan rana da karfe 7, dakarun da ke dauke da makamai kimanin 2000 sun kai hari ga wani sansanin UNMISS da ke birnin Akobo na jihar Jonglei na kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kiyaye zaman lafiya 'yan asalin India guda 2 tare da fararen hula a kalla 11. (Bako)