Ta kuma kara da cewa, kasar Sin tana kira ga bangarorin biyu da rikicin ya shafa da su mai da hankali kan moriyar kasar da kuma jama'arta,su yi kokarin warware rikicin da ake fuskanta a kasar ta hanyar shawarwari bisa fatan gamayyar kasa da kasa.
Bugu da kari, ta bayyana cewa, tun lokacin da rikici ya barke a kasar Sudan ta Kudu, kasar Sin ta yi kokari sosai wajen ciyar da aikin gudanar da shawarwarin zaman lafiya a kasar gaba, kuma nan gaba kadan, kasar Sin tana fatan ci gaba da tuntubar bangarorin da abin ya shafa, don ganin an shimfida zaman karko a kasar cikin sauri. (Maryam)