Wakiliyar musamman ta babban sakataren MDD a kasar Sudan ta Kudu Hilde Johnson, ta yi kira ga daukacin masu fada a ji da su gaggauta tabbatar da daukar matakan dawo da yanayin zaman lafiya da lumana a Sudan ta Kudu.
Johnson wadda ta bayyana hakan ga manema labaru jiya Alhamis 26 ga wata, ta kuma bayyana cewa, kamata ya yi banbance-banbancen dake tsakanin al'ummar kasar, su zamo hanyar karfafar juna ba wai rarrabuwa ba.
Daga nan sai ta yi fatan fara hallarar karin dakarun wanzar da zaman lafiya karkashin tawagar UNMISS cikin kwanaki biyu daga Alhamis.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai kwamitin tsaron MDD ya amince da bukatar kara yawan dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar. Don gane da hakan, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya ce, za a samar da karin sojoji 5,500, da kuma 'yan sanda 423 daga rundunonin MDDr da na kungiyar AU, dake kasashen jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Cote d'Ivoire, da Liberia, kuma da yankunan Darfur da Abyei dake kasar Sudan.
Rikicin kasar ta Sudan dai ya sabbaba rasuwar mutane sama da 1,000, baya ga wasu dubbai da suka rasa matsugunnansu. (Saminu)