Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni a ranar Litinin din nan 30 ga wata ya ce, shugabannin kungiyar samun cigaba tsakanin gwamnatoci za su hada hannu su yaki sojojin magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Reik Machar idan har ya ki amincewa ya karbi tayinsu na dakatar da bude wuta.
Kamar yadda kafar yada labarai ta kasar Sudan ta ruwaito, kuma kamfanin dillancin labaran Xinhua ta aiko mana, an ce, kungiyar za ta samu galaba a kan Machar domin hana yaduwar tashin hankalin da yanzu haka ake fuskanta a sabuwar kasar.
Shugaba Museveni ya bayyana a Juba, babban birnin kasar cewa, sun bai wa Reik Machar kwanaki hudu, kuma idan har bai bi wannan shawara ba, to za su neme shi a yadda kungiyar ta tsai da lokacin taronta.
Tun da farko dai gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta sanar da amincewarta ta dakatar da bude wuta, amma Machar ya ki amincewa, yana mai cewa, sai an samar da hanyar da za'a zuba ido a ga yadda dakatar da bude wutan zai kasance. (Fatimah)