Ofishin tsare-tsare na hukumar ba da agajin jin kai ta MDD ko OCHA a takaice, ya ce, kungiyoyin ba da agaji dake aiki a kasar Sudan ta Kudu, na bukatar tallafin kudade da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 166, don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ofishin kakakin MDD wanda ya rawaito wannan batu, ya ce, ana fatan yin amfani da wadannan kudade ne, wajen ayyukan da suka jibanci kare rayukan al'ummun da tashe-tashen hankula da ke wakana yanzu haka a Sudan ta Kudu suka ritsa da su.
An ce, ana sa ran kashe wadannan kudade wajen samar da tsaftataccen ruwan sha, da samar da kayan kiwon lafiya da kuma aikin lura da matsugunnan wucin gadi da dai sauran muhimman ayyuka.
Wannan kudade dai bangare ne na jimillar kudin da yawansa ya haura dala miliyan dubu daya da dari daya, da ake fatan kashewa cikin shekara mai zuwa, domin ba da tallafi ga daukacin masu bukata a kasar.
Da yake karin haske kan wannan lamari, jami'in shirye-shirye na hukumar ta OCHA a kasar Sudan ta Kudun Toby Lanzer, ya ce, akwai matukar bukatar samar da wadannan kudade, muddin ana da burin kare rayukan fararen hula cikin watanni masu zuwa.
A yanzu haka dai kasar Sudan ta Kudu, na fama da rikicin siyasa da ya sanya kimanin mutane sama da 90,000 rasa matsugunnansu, yayin da kuma wasu kusan 58,000 suke fakewa a sansanin tawagar MDD dake kasar. (Saminu)