in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na nuna damuwarta sosai kan rikicin Sudan ta Kudu
2013-12-26 10:29:52 cri

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na tarayyar Afrika AU, da ya yi taronsa a ranar Laraba kan rikicin kasar Sudan ta Kudu ya bayyana babbar damuwarsa kan tsanancewar halin da ake ciki a cikin wannan matashiyar kasa dake nahiyar Afrika a cikin wata sanarwa ta wannan gamayyar Afrika.

Kwamitin ya yi kashedi kan bazuwar rikici a kasar Sudan ta Kudu da ya taso daga rigimar siyasa zuwa wani yaki da makamai dake neman canjawa zuwa na tashe-tashen hankalin kabilanci da na yakin basasa, in ji wannan sanarwa.

Kwamitin ya bayyana takaici da mamakin ganin wannan karamar kasa dake Afrika take kokarin fadawa cikin wani kazamin rikicin cikin gida, da kasawar shugabannin siyasa wajen amsa bukatu da fatan jama'ar kasar da kuma amsa fata da taimakon da kasashen Afrika da gamayyar kasa da kasa suka bayyana.

Hakazalika, kwamitin ya yi allawadai da hare-hare kan fararen hula dake shafar gungun kabilu da sauran al'ummomi, da ayyukan keta hakkin dan adam, musamman ma kan mata da kananan yara da masu raunin zaman rayuwa.

A karshe, kwamitin na AU ya soki lamarin harin da aka kai kan sansanin MDD dake Sudan ta Kudu a ranar 19 ga watan Disamba da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin MDD biyu, tare da yin kira ga bangarorin da ba su ga maciji da juna a kasar Sudan ta Kudu da su nuna kishin kasa da hangen nesa domin moriyar kasarsu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China