Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bukaci cikakken hadin kai daga dukkan bangarori dake arangama da juna a kasar Sudan ta Kudu a kokarin samar da maslaha a kasar.
Mr. Ban a cikin hirar da ya yi da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit ta wayar tarho a ranar Litinin din nan, ya kuma yi maraba da kokarin da shi shugaba Kiir ke yi na ganin an tattauna tsakanin shi da jagoran 'yan adawa, yana mai ba shi shawarar da ya tabbatar da sakin fursunonin siyasa ba tare da bata lokaci ba.
A bayanin da ofishin kakakin magatakardar Ban ya ce, majalissar a shirye take ta ba da duk goyon bayan da ya kamata ga kungiyar cigaban kasashen kudancin Afrika IGAD wajen shiga tsakani domin a samar da zaman lafiya, yana mai kira ga dukkan bangarori da su ba da hadin kai wajen samar da maslaha a kasar.
Mr. Ban har ila yau ya jaddada bukatar dake akwai ga wadanda suka kai hari a kan fararen hula da su dauki alhaki a kan wuyansu. (Fatimah)