Bisa labaran da kafofin watsa labarai na kasar Sudan ta Kudu suka bayar, an ce, shugabannin uku sun yi shawarwari a asirce. Cikin wata sanarwar da ministar harkokin wajen kasar Kenya Amina Mohamed ta bayar wadda ita ma ta ziyarci kasar Sudan ta Kudu tare da shugaban kasarta ta Kenya, an ce, shugaba Kenyatta ya kai ziyara kasar Sudan ta Kudu ne don ganin an warware ricikin kasar bisa fatan gwamnatocin yankin.
Bugu da kari, bisa labarin da aka samu daga shafin intanet na "Sudan tribune", an ce, tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Machar wanda shugaba Salva Kiir Mayardit ya zarga da shirya juyin mulki ya bayyana cewa, ya riga ya shirya wata tawaga da za ta tattauna da shugaba Salva Kiir Mayardit. Kuma labarin ya ruwaito jami'an gwamnatin kasar na cewa, a ran 31 ga watan Disamba, wakilan gwamnatin kasar Sudan ta Kudu da na kungiyar da ke adawa da gwamnatin dake karkashin jagorancin Riek Machar za su yi shawarwari kai tsaye a babban birnin kasar Habasha, Addis Ababa, kuma kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka ta IGAD ce za ta jagoranci taron shawararin da zu yi a tsakaninsu. (Maryam)