in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya jajanta wa takwaransa na Rasha kan harin da aka kai a birnin Volgograd
2013-12-30 19:19:33 cri
A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga waya ga takwaransa na Rasha, Vladimir Putin domin nuna jajantawa kan jerin hare-haren ta'addanci da aka kai a birnin Volgograd na kasar ta Rasha, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwa tare da jikkatar mutane da dama.

A wannan rana kuma, firaministan Sin Li Keqiang shi ma ya buga waya ga takwaransa na Rasha Alexander Medvedev kan wannan batu.

Bugu da kari, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin Qin Gang ya bayyana a yau a nan birnin Beijing cewa, da babbar murya Sin ta yi Allah wadai da jerin hare-haren ta'addanci da aka kai a birnin Volgograd da ke kudancin kasar Rasha.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China