in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shawarwari karo na 12 dake tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Sin, Rasha, da India
2013-11-11 09:09:39 cri
A ranar 10 ga watan Nuwamba, a birnin New Delhi da ke kasar India, an yi shawarwari karo na 12 na ministocin harkokin waje na kasashen Sin, Rasha, da India, inda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov da na kasar India Salman Khurshid

A yayin shawarwarin, Wang Yi ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Sin, Rasha, da India, su yi la'akari wajen inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen uku bisa manyan tsare-tsare kuma ta fannoni 3, wadanda suka kunshi amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare, da daidaita manyan lamuran duniya don kiyaye moriyarsu, a sa'i daya kuma, da sa kaimi ga raya dangantakar kasa da kasa bisa tsarin demokuradiyya, da zurfafa hakikanin hadin gwiwa, ta haka ne, wadannan kasashen uku za su taka muhimmiyar rawa game da manyan batutuwan duniya da shiyya-shiyya.

Haka kuma, ministocin harkokin waje uku sun yi musayar ra'ayi game da batutuwan duniya da na shiyya-shiyya da aka dora muhimmanci sosai a kai, inda suka amince da inganta hadin gwiwa da ke tsakaninsu a M.D.D., rukunin kasashen G20, da kasashen BRICS, da taron kasashen Asiya da Turai, da kungiyar SCO da sauransu, don karfafa yunkurin lalata makamai masu guba a Siriya da warware rikicin siyasan kasar, da shirya taron kasa da kasa na Geneva karo na 2 cikin hanzari, da ci gaba da warware batun nukiliya na kasar Iran daga manyan fannoni kuma cikin lokaci, da nuna goyon baya game da yunkurin samar da zaman lafiya a Afghanistan, don taimakawa kasar ta samu zaman lafiya da ci gaba, da warware batun nukiliya na zirin Koriya ta Arewa, da gaggauta farfado da shawarwari na bangarorin nan 6 ba tare da bata lokaci ba. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China