Shugaban kungiyar sada zumunta a tsakanin Amurka da Sin Qiao Fengxiang ya yi tsammani cewa, harin da aka kai a jihar Xinjiang a kwanakin baya ba matsalar kabila ko addini ba ce, yaki ne dake tsakanin 'yan aware da masu yaki da 'yan aware, da kuma tsakanin masu tada zaune tsaye da masu tabbatar da dinkuwar kasar Sin. Hare-haren ta'addanci sun haddasa mutuwa da raunatar jama'a tare da hasarar dukiya. Sinawa dake kasashen waje sun nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Sin da ta tabbatar da zaman lafiya, daukar matakai masu dacewa, yaki da dukkan ayyukan ta'addanci, da kuma kiyaye zaman lafiya da tabbatar da tsaron jama'a da dukiyarsu a jihar Xinjiang.
Mataimakin shugaban kungiyar sa kaimi ga samun zaman lafiya da dinkuwar kasar Sin dake kasar Rasha Yuan Yi ya bayyana cewa, Sinawa dake kasar Rasha sun yi fushi sosai ga hare-hare da ayyukan kawo illa ga hadin kai da zaman lafiya a jihar Xinjiang da 'yan ta'addanci suka yi. Sinawa dake kasashen waje ciki har da Sinawa dake kasar Rasha suna nuna goyon baya ga tabbatar da dinkuwar dukkan kasar Sin. (Zainab)