Birnin Kashgar yana wani muhimmin wuri a yankin kudancin jihar Xinjiang, wanda ke makwabtaka da kasashe da dama da ke yankunan tsakiya da kudancin Asiya, kuma yana da hukumomin kwastam guda 5 don bude kofa ga kasashen waje.
Bikin baje-kolin kayayyakin Kashgar ya zamanto wani muhimmin biki da ya gudana ne har sau 9, a wannan shekara kuma, an jawo hankalin 'yan kasuwa na kasashe 8 da ke makwabtaka da jihar Xinjiang, ciki har da Pakistan da Tajikistan da kyrgyzstan, da kuma 'yan kasuwa da suka fito daga larduna da jihohi daban daban na gida, don su halarci bikin.
A cikin shekaru 3 da suka gabata, yawan kudin da aka samu a birnin Kashgar wajen aikin samar da kayayyaki ya wuce kudin Sin Yuan biliyan 50, kuma matsakaicin saurin karuwa da aka samu ya kai kashi 16.6 cikin 100 a kowace shekara.(Bako)