in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta amince da kudurin da shugabannin gabashin Afirka suka tsayar kan batun Sudan ta Kudu
2013-12-29 17:16:40 cri
Jiya Asabar 28 ga wata, wakilin musamman mai kula da harkokin nahiyar Afirka na kasar Sin Zhong Jianhua ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali sosai kan rikicin da ke faruwa a kasar Sudan ta Kudu, kuma ta nuna goyon baya kan kudurin da kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka ta IGAD ta tsayar kan batun kasar Sudan ta Kudu.

Mr. Zhong ya bayyana cewa, kasashen gabashin Afirka sun yi allah wadai da a mai da rikicin siyasa a matsayin rikicin kabilu da na addinai, a yayin taron koli na kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka ta IGAD, an yi kira da a tsayar da rikice-rikice a kasar Sudan ta Kudu, kuma a halin yanzu ana damuwa sosai kan rikice-rikicen da watakila za su bazuwa a tsakanin wasu kabilun kasar Sudan ta Kudu.

Mr. Zhong ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana son ba da taimako wajen kawo karshen tashen hankulan jama'ar kasar Sudan ta kudu, da kuma ciyar da aikin shimfida zaman karko a kasar Sudan ta kudu gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China