in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bukaci a warware rikicin Sudan ta Kudu cikin lumana
2013-12-26 09:54:22 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya jaddada bukatar warware rikicin siyasar kasar Sudan ta Kudu cikin lumana.

Mr. Ban wanda ya bayyana hakan yayin wani jawabi da ya gabatar a matsayin sako ga al'ummar kasar a ranar Laraba, ya ja hankalin masu ruwa da tsaki a rikicin dake nema ya wargaza wannan sabuwar kasa, da su kaucewa daukar dukkanin matakai da ka iya rura wutar rikici.

Babban magatakardar MDDr ya kuma ce, duk da mawuyacin halin da Sudan ta Kudun ke ciki, a hannu guda tana da kawaye dake da aniyar tallafa ma ta. Ya ce, kwamitin tsaron MDD ya zartas da kudurin kara yawan dakarun wanzar da zaman lafiya, da suka hada da sojoji da 'yan sanda, a yunkurin da ake ci gaba da yi na daidaita harkokin tsaron kasar.

Tashe-tashen hankula dai na kara kamari a Sudan ta Kudu, tun daga 15 ga watan nan da muke ciki, sakamakon yunkurin juyin mulki, da gwamnatin shugaba Salva Kiir ta ce, sojoji masu biyayya ga korarren mataimakinsa Riek Machar, suka yi yunkurin aiwatarwa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China