Babbar jami'ar hukumar kare hakkin bil'adama ta MDD Navi Pillay, ta bayyana damuwa kan mummunan yanayin da kasar Sudan ta Kudu ke ciki a hakin yanzu.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, Pillay, ta ce, akwai rahotanni dake nuna yadda ake ci gaba da aikata laifuka masu alaka da kisan rayuka da keta hakkokin dan adam a kasar. Don haka ta yi kira ga daukacin masu fada a ji dake kasar, da su kauracewa rura wutar rikici.
Ta ce, a baya bayan nan an gano wani wagegen kabari da aka binne mutane masu yawa cikin sa a garin Bentiu, baya ga rahoton wasu makamantan sa biyu, da aka ce an samu a birnin Juba, helkwatar kasar.
Har wa yau Pillay, ta bayyana damuwarta don gane da halin da mutanen da gwamnatin kasar mai ci ta tsare ke ciki, wadanda suka hada da daruruwan fararen hula da aka cafke a birnin Juba. Ta kuma yi kira ga kasashen duniya da su ba da agajin da ya dace, domin kare rayukan fararen hular kasar.
Rikicin siyasar kasar Sudan ta Kudu dai na ci gaba da kazanta tun daga makon jiya, bayan da fada ya kaure tsakanin tsagin sojojin kasar biyu, wato magoya bayan shugaba Kiir daga kabilarsa ta Dinka, da kuma masu 'yan kabilar Nuer ta korarren mataimakin shugaban kasar Riek Machar. (Saminu)