A ranar 7 ga wata, wakilan kasashe shida masu ruwa da tsaki kan batun nukiliyar kasar ta Iran, watau Amurka, Burtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus da wakilin kasar ta Iran sun fara wani sabon zagaye na yin shawarwari tsakaninsu wanda bisa jadawalin da aka tsara, za a kammala cikin kwanaki biyu. Sai dai bayan kammala shawarwari a ranar ta daya, ta bakin kakakinta, babbar wakiliya mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro ta tarayyar kasashen Turai Catherine Ashton ta bayyana cewa, a halin yanzu, kasashe shida da kasar Iran na dukufa wajen tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran din, tana kuma fatan za a iya samun ainihin ci gaba kan batun, idan har kasar Iran din za ta iya yin alkawari, da zai baiwa watakila kasashe shida damar sa hannu kan yarjejeniyar da za a cimma.
Yayin da ake ci gaba da tattaunawa a hannu guda a ran 8 ga wata, firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ba da wata sanarwa, da ke kunshe da nuna matukar kiyayarsa ga dukkan yarjejeniyoyin da kila kasashe shida za su kai ga sanyawa hannu yayin taron shawarwarin da ake yi. (Maryam)