Bisa labarin da aka samu, an ce, cikin 'yan kwanaki masu zuwa, Mr. Brahimi zai gana da shugaba Bashar al-Assad da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar da kuma wakilan 'yan adawar kasar. Kuma ana saran yayin ganawarsa da wakilan 'yan adawa, zai ba da shawara ga 'yan adawa ta cikin gida da wadanda ke ketare da su kafa wata tawagar hadin gwiwa don halartar taron na Geneva karo na biyu inda za a tattaunawa kan yadda za a warware matsalar kasar ta Syria. (Maryam)