in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata Japan ta mutunta jama'ar sauran kasashe, in ji Ban Ki-Moon
2013-12-28 16:59:08 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya yi wani tsokaci kan ziyarar da firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya kai Haikalin Yasukuni, inda ya jadada cewa, kamata yayi kasar Japan, ta mutunta jama'ar sauran kasashe, musamman ma wadanda suka sha fama da yakin duniya na biyu, ta kuma mai da hankali ga kafa dangantakar abokantaka cikin aminci tsakaninta da kasashen nahiyar gabashi da na Arewacin Asiya.

Bugu da kari, Mr. Ban wanda ya bayyana hakan ta bakin kakakinsa ya ce, shugabannin kasa da kasa da ragowar masu ruwa da tsaki, na da muhimmiyar rawa da zasu iya takawa kan wannan batu. Mr Ban ya ce, Sin da Korea ta kudu sun mai da martani sosai kan ziyarar ta firaminista Abe. Daga nan sai magatakardar MDDr ya bayyana matukar takaicin sa don gane da yadda dangantakar dake tsakanin wadannan kasashe ta yi tsimi saboda wannan dalili mai alaka da tarihi, tare da fatan kasashe za su dauki matakan cimma matsayi guda, su kuma karfafa fahimtar juna kan wannan batu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China