Wasu kafofin yada labarun Japan din sun yi shelar cewa, nufin Japan da Rasha na shirya irin wadannan shawarwari shi ne dakile ci gaban kasar Sin, sai dai nan take Sin da Rasha sun musunta hakan. Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, babu wanda zai iya kawo cikas ko lalata bunkasuwar dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Rasha daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare. Ta ce, wasu na yunkurin haddasa tunzuri a tsakanin Sin da Rasha, tabbas ne hakarsu ba za ta tarar da ruwa ba.
Har wa yau kuma, Morgulov Igor, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha shi ma ya musunta irin wancan hasashe da wasu kafofin yada labaru na Japan suka yi. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin, abokiyar kasar Rasha ce a fagen hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. Ya ce, asarsa ta Rasha ba za ta ci dunduniyar kasar Sin a asirce ba.(Tasallah)