in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci daukar makatan shawo kan matsalar da tashar nukiliyar Fukushima ke haifarwa
2013-11-06 10:52:35 cri

Mahukuntan kasar Sin sun bukaci kasar Japan, da ta gaggauta daukar matakan da suka wajaba, domin dakile matsalar yoyon da tashar nukiliyar nan ta Fukushima ka iya haifarwa.

Mataimakin wakilin din din din na kasar Sin a MDD Wang Min ne ya yi wannan kira, yayin babban taron majalissar da aka gudanar kan rahoton hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.

Wang Min ya kara da bayyana bukarar samarwa kasar ta Japan tallafin shawo kan matsalar yoyon da tashar ta Fukushima ke yi, lamarin da ke gurbata ruwa dake kewayen ta.

Haka zalika wakilin kasar ta Sin ya bukaci hukumar ta IAEA, da ta tabbatar ana aiwatar da tsare-tsaren kare aukuwar hadurra, masu alaka da makamashin nukiliyar da kasashen duniya ke amfani da shi, domin cimma burin bunkasuwa, da ci gaban sashen sarrafa wannan makamashi.

Ya ce, duk da kasancewar kasar ta Sin daya daga manyan kasashen dake amfani da makamashin na nukiliya, a hannu guda kasar na dora muhimmanci, ga batun kandagarkin aukuwar hadurra daka iya bijirowa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China