in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Japan da ta duba ayyukanta a lokacin cika shekaru 70 na sanarwar Alkahira
2013-12-03 11:02:23 cri

A ranar Litinin 2 ga wata, kasar Sin ta bukaci kasar Japan da ta fuskanci tare da duba ayyukanta a hakikance na tarihin kai mamaya da ta yi, a wannan watan da aka cika shekaru 70 da sanar da yakin duniya na biyu.

Ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei, Sin tana bukatar kasar ta Japan da ta fuskanci tare da duba ayyukan da ta yi lokacin da ta kai mamaya, ta mutunta kalamanta tare da cika su a idon duniya domin sake samun amincewa daga makwabtanta dake nahiyar Asiya da ma duniya baki daya.

Hong Lei ya nuna cewa, sanarwar Alkahira wadda ita ce ta ba da damar nasarar da aka samu a yakin duniya na 2, da kuma shirya muradun bayan yaki, wani kundi ne da duniya ta amince da shi a hukunce tare da dora muhimmanci a kai.

Ya ce, bikin saka hannu a wannan kundi wata alama ne ta cigaba da mutunta zaman lafiyar da aka samar, daidaito da cigaba a yankin Asiya da fasifik da ma sauran kasashen duniya baki daya.

Hong Lei ya jaddada cewa, wannan sanarwa ta samar da kundin bisa doka mai muhimmanci game da dokokin duniya da suka shafi kasar Sin wajen karbo yankunan da sojojin Japan suka kwace ko kuma suka sace bayan yakin duniya na 2. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China