Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi maraba da kudurin da kwamitin tsaron MDDr ya cimma, na kara yawan dakarun wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudun.
Da yake bayyana hakan jim kadan da kammala zaman kwamitin na ranar Talata 24 ga watan nan, Ban ya ce, yanzu haka an amince a kara yawan dakarun sojin majalissar zuwa 12,500, ba ya ga jami'an 'yan sanda da za a kara adadinsu zuwa 1,323. Babban magatakardar MDDr ya kara da cewa, daukar wannan mataki zai karfafa yunkurin da ake yi na baiwa rayukan fararen hula kariya. Daga nan sai ya yi kira ga daukacin bangarorin masu ruwa da tsaki a kasar ta Sudan ta Kudu, da su kai zuciya nesa, su kuma kauracewa daukar dukkanin wani mataki da ka iya rura wutar rikici.
A nasa tsokaci, manzon kasar Sudan ta Kudu a MDD Francis Mading Deng, yabawa yunkurin da kasashen duniya ke yi ya yi, don gane da dawainiyar ganin dorewar sabuwar kasar Sudan ta Kudu.
Sudan ta Kudu wadda ta samu 'yancin kai cikin watan Yulin shekara ta 2011, a yanzu haka na fama da rikicin siyasa, wanda ya sanya kimanin mutane sama da 80,000 rasa matsugunnansu, yayin da kuma wasu kusan 45,000 suke fake a sansanin tawagar MDD ta UNMISS dake kasar.
Ana dai danganta rikicin siyasar kasar ne da zargin da shugaba Salva Kiir ya yiwa korarren mataimakinsa Riek Machar, na shirya juyin mulkin da bai yi nasara ba, lamarin da kuma ya juye zuwa fadan kabilanci tsakanin manyan kabilun kasar biyu mafiya girma wato Dinka da Lou Nuer. (Saminu)